Babban batu da ake tattauna a wannan karo shi ne, burin samun bunkasuwa, ana kuma mai da hankali kan batun zuba jari, da gina manyan ababen more rayuwa, da kalubalen da ake fusakanta yayin samun bunkasuwa, yin kwaskwarima kan asusun ba da lamuni na IMF, da sa ido kan harkokin kudi, da kuma aiwatar da hadin kai a fannin haraji da gudanar da sauye-sauye.
Da safiyar wannan rana ne ministan harkokin wajen kasar Austriliya Joe Hockey, ya kira wani taron manema labaru, inda ya bayyana cewa, yayin wani taron da aka gudanar kwanaki biyu da suka gabata, mahalartansa sun cimma matsaya, tare da bayyana aniyar warware wasu batutuwa. Yace ya yi imanin cewa, za a samu ci gaba mai ma'ana yayin wannan sabon taro.
Bugu da kari, a yammacin wannan rana, ministocin kudi, da shugabannin manyan bankunan kasa da kasa, za su yi taro a asirce, domin musanyar ra'ayi, kan babban taken taron, wato "Halin da tattalin arzikin duniya ke ciki". Har wa yau a daren wannan rana za a yi shawarwari kan yadda za a dauki matakan ba da tabbaci, ga samun isashen jari daga bangarori daban-daban, domin gina manyan ababen more rayuwa a duniya. (Amina)