A jawabin da ya gabatar yayin taron manema labarai, ministan kudi na kasar Australia Joe Hockey ya sanar da rufe taron, inda ya gabatar da sanarwar bayan taron da ke bayyana fatan samun bunkasuwa da dorewar tattalin arzikin duniya nan ba da dadewa ba.
A cewar sanarwar bayan taron da kungiyar ta amince da shi, ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kungiyar ta G20, sun himmatu wajen aiwatar da manufofin da za su taimaka wajen ci gaban alkaluman GDP na sama da kashi 2 cikin 100, adadin da ya haura abin da ake fatan samu cikin shekaru biyar masu zuwa.
Sanarwar ta ce, an bullo da manufofin ne da nufin samar da karin dala tiriliyan 2 a ayyukan tattalin arzikin duniya da karin miliyoyin guraben aikin yi.
Bugu da kari, kasashen na G20 sun yi alkawarin daukar kwararan matakan bunkasa harkokin cinikayya, takara, sadarwa, guraben aiki yi da zuba jari, musamman a bangaren kayayyakin more rayuwa da kuma samar da tabbaci a kasuwannin kudi. (Ibrahim Yaya)