in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na goyon bayan taron koli na G20 da ya yi alkawarin tsara taswira ta shawarwarin Doha
2013-09-03 11:04:05 cri

Bisa gayyatar da aka yi masa, a ranar 2 ga wata ministan cinikayya na kasar Sin, Gao Hucheng ya buga waya ga sabon babban daraktan kungiyar WTO, Roberto Azevedo, inda ya bayyana cewa, kasar Sin na goyon bayan shugabannin da za su halarci taron koli na G20 da su daddale yarjejeniya game da shirin "Early Harvest Program" a yayin taron ministoci karo na 9 na kungiyar WTO, domin yin alkawari mai tabbaci kan tsara taswirar shawarwarin Doha.

Shirin "Early Harvest Program" na Doha, shiri ne na kungiyar WTO game da gaggauta yafewa kasashe 48 mafiya talauci harajin safarar kayayyaki, wanda aka kaddamar a shekarar 2011, kasashen da suka fi samun saurin karuwar tattalin arziki, ciki har da Sin da India da sauransu sun mayar da martani mai yakini kan shirin, amma ba a cimma matsaya a kai ba tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Bayan haka kuma, Gao Hucheng ya nuna yabo ga muradin Azevedo na inganta shawarwarin Doha, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan kungiyar WTO da na babban daraktan kungiyar.

A nasa bangaren kuma, Azevedo ya bayyana cewa, yanzu shawarwarin Doha na cikin wani mawuyacin hali, don haka zai inganta shawarwarin ta hanyar shigar da shugabanni a ciki sannu a hankali, yana kuma da shirin kiran wani taron ministoci a 'yan kwanaki masu zuwa, kana yana fatan Sin za ta halarci shawarwarin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China