Yayin taron manema labaran da cibiyar watsa labaran tawagar wakilan kasar Sin ta kira, Qin Gang ya nuna cewa, kasar Sin ta damu matuka kan halin da kasar Syria take ciki a yanzu. Kuma Sin ba ta amincewa ko wace kasa, ko wata kungiya, ko wane mutum ya yi amfani da makamai masu guba. Abu mafi muhimmanci a halin yanzu shi ne, MDD ta dukufa wajen yin bincike kan zargin amfani da makamai masu guba, ta yadda za a iya gano gaskiya, kafin daukar ko wane irin mataki a nan gaba.
Qin Gang ya kuma kara da cewa, ba za a iya warware matsalar da ake fama da ita ta hanyar yaki ba. Ya ce a halin yanzu ya kamata kasashen duniya su dukufa matuka wajen dakile tashe-tashen hankula a kasar Syria, tare da kuma ba da taimako wajen aiwatar da sauyin siyasa a kasar. (Maryam)