Kamar yadda shugaban sashin tattalin arziki na kasa da kasa a ma'aikatar harkokin wajen kasar Zhang Jun ya shaida ma manema labarai a alhamis din nan, ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron karo na 9 na shugabannin kungiyar G20 da za'a yi a birnin Brisbane na kasar Australiya. tsakanin ranakun 15 zuwa 16 ga watan nan na Nuwamba.
Mr. Zhang ya kara da cewa a lokacin taron shugaba Xi zai yi bayanin matsayar kasar game da manyan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya, zai kuma bada shawarwari, da tayin kara hadin gwiwa a wannan taron.
Xi Jinping zai yi aiki tare da sauran mambobin kungiyar domin samar da hanyar samar da cigaba, inganta rayuwar jama'a da kuma kara azama ga tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya.
A wani bangaren na taron G20 kuma, shugaba Xi Jinping zai halarci taron kasashen BRICS wato kasashen Brazil,Rasha,India,Sin, da kuma Afrika ta kudu.(Fatimah)