in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya ba da shawarar inganta dangantakar tattalin arziki da yankin tsakiyar Asiya
2013-09-07 20:34:26 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a samar da tsare-tsaren da za su inganta hadin gwiwa da cudanyar tattalin arziki tsakanin kasarsa da kasahen dake yankin tsakiyar nahiyar Asiya.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabin da ya gabatar a jami'ar Nazarbayev dake birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar Asabar din nan. Ya ce, akwai bukatar kasashen dake wannan yanki su karfafa batun musayar bayanai, da inganta hadin kai a fagen tsara manufofi da dokokin bunkasa tattalin arziki.

Da yake bayyana matsayin kasar Sin don gane da alakarta da sauran kasashe makwafta, Xi ya ce, kasarsa ba ta da niyar yin shisshigi cikin al'amuran cikin gidan ragowar kasashe, hakan a cewarsa, ya dace da manufar martaba 'yancin kai, da na ikon fid da manufofin kashin kai da ko wace kasa ke da shi.

Bugu da kari shugaban kasar ta Sin ya yi alkawarin cewa, kasarsa za ta ci gaba da inganta alakar abokantaka da aminci tsakaninta da ragowar kasashen dake tsakiyar Asiya. Har ila yau shugaba Xi ya yi kira da dukkanin sassan da wannan batu ya shafa da su marawa juna baya, don gane da bukatar kare martabar juna, da tsaro da sauran muhimman bukatu. Acewarsa hakan zai ba da kyakkyawar damar yaki da manyan matsalolin dake addabar nahiyoyin duniya, cika had da ayyukan ta'addanci, da na masu tsattsauran ra'ayi, da safarar miyagun kwayoyi, da dai sauran manyan laifuka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China