in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagoran kungiyar IS ya ji rauni, in ji Iraki
2014-11-10 16:45:35 cri

Gidan telibijin na kasar Iraqi ya ba da labari cewa, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Iraki ta tabbatar a ran 9 ga wata cewa, babban jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ya ji rauni a harin da aka kai masa, baya ga sauran jagororin kungiyar da dama da suka mutu.

Hukumar tsaro ta lardin Nineveh na kasar Iraki ta ba da labari a ran 9 ga wata cewa, a daren ranar 7 ga wata, dakarun kawancen da ke yaki da kungiyar IS karkashin jagorancin kasar Amurka sun kai jerin hare-hare ta sama kan birnin Mosul hedkwatar lardin, inda jiragen saman yakin suka harba rokoki kan ayarin motocin da ake zaton suna dauke da babban jagoran kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi.

An ba da labari cewa, Abu Bakr al-Baghdadi shi ne shugaban kungiyar ta IS, wadda ke rike da yankunan arewacin kasar ta Iraki da wasu wuraren dake arewa maso gabashin kasar Sham.

Tun a watan Nuwamban shekarar 2011 ne majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta yi tayin bayar da ladan dala miliyan 10 ga duk wanda ya samar da bayanan da za su taimaka wajen cafke Abu Bakr al-Baghdadi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China