Batun ko za a kara kai hari ta sama, ko tura rundunonin soja na kasa ko shata yankunan hana zirga-zirgar jiragen sama bisa shawarar kasashen Faransa da Turkiya, su ne batutuwan da za a tattauna a taron. A jiya da yamma ne, shugaba Barack Obama na kasar Amurka ya gana da wadannan shugabannin soja na kasashe daban daban. Masu sa ido kan al'amura na cewa, wannan mataki ne da ke bayyana matsayin kasar Amurka. Bugu da kari, yadda za a iya daidaita matsayin kasashen da ke cikin wannan kawance shi ne wani muhimmin batun da ke jawo hankulan jama'a.
Madam Susan Rice mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro ta gaya wa manema labaru cewa, bangaren Turkiya ya goyi bayan kasar Amurka da sauran kasashen da ke cikin wannan kawance su yi amfani da sansanin sojan kasar domin su yaki dakarun ISIS. (Sanusi Chen)