A yayin ganawar, Fallon ya nuna yabo ga sojojin kasar Iraki game da wasu nasarorin da suka samu na kwace wasu yankuna daga hannun IS, kana ya jaddada cewa, kasar Britaniya za ta samar da makamai da masu horar da ma'aikata ga sojojin kasar Iraki.
Bayan da ministan harkokin wajen kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Iraki Bashar Jaafari a ranar 5 ga wata, Cavusoglu ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, kasar Turkiya na fatan gwamnatin kasar Iraki za ta hada kan kungiyoyi daban daban wajen yaki da kungiyar IS tare, kasar Turkiya za ta taimakawa kasar Iraki wajen horar da sojoji. A nasa bangare, Jaafari ya bayyana cewa, yakin da sojojin kasar Iraki suka yi da kungiyar IS shi ne aikin cikin gida na kasar, kasar Iraki tana maraba da sauran kasashe da suka bada gudummawa, amma ta ki amincewa da sauran kasashen waje da su tura sojojinsu zuwa kasar Iraki.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gudanar da taron manema labaru a fadar White House a ranar 5 ga wata, inda ya maida aikin neman samun iznin yaki da kungiyar IS a matsayin daya daga cikin bukatunsa uku a yayin da yake yin hadin gwiwa tare da majalisar dokokin kasar. (Zainab)