in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta kashe 'yan Sunni 36 a kasar Iraki
2014-11-04 11:01:26 cri
Wani jami'in hukumar tsaron kasar Iraki ya bayyana cewa, kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci ta IS ta kashe 'yan Sunni 36, ciki hadda mata da yara kanana, a birnin Heet na jihar al-Anbar dake yammacin kasar Iraki.

Jami'in ya kuma bayyana cewa, an gano wani wuri da aka binne gawawwaki 36 na 'yan kabilar Albu Nimer, a wajen birnin Heet, wadanda suka hada da yara biyu da mata 4.

Bisa labarin da hukumar tsaron kasar Iraki ta bayar, an ce, sojojin gwamnatin kasar sun cimma nasarar fatattakar dakarun kungiyar ta IS, wadanda suka kai hari ga kamfanin samar da mai na Baiji a ranar 3 ga wata, kana sojojin sun harbe dakarun 14. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China