Kakakin hedkwatar sojan kasar Amurka ya shedawa manema labaru a ran 8 ga wata cewa, kawancen dakile kungiyar IS a karkashin jagorancin Amurka ya kai hari kan ayarin motocin IS a daren ran 7 ga wata a kusa da birnin Mosul na kasar Iraqi. Ya ce, wannan ayarin motoci ya kunshi kusoshin IS da dama, amma ba a san ko babban jagoran IS Abu Bakr al-Baghdadi na ciki ba ko a'a.
Kakakin ya ce, wannan ayarin motoci 10 na dauke da kusoshin IS da dama wadanda suka yi shirin yin shawarwari a yankin Mosul a wannan rana. Ya zuwa yanzu, ba a san ko babban kusanta Abu Bakr al-Baghdadi yana cikin wadannan motoci ko a'a ba. Ban da haka, a cewarsa, sojin Amurka da sojojin kawancen sun kai hari daga sama kan garin al-Qaim a daren ran 7 ga wata, matakin da ya murkushe motocin yaki da dama da tasoshin bincike biyu.
Jami'in yankin Mosul ya bayyana cewa, harin da sojin Amurka da sojin kawancen suka kai ya yi sanadin mutuwar 'yan ta'addan IS 50. Har wa yau, wani mutum da ya ganewa idansa lamarin a yankin al-Qaim ya ce, a kalla mutane 15 sun mutu cikin harin, yayin da wasu 31 suka raunuka. (Amina)