Sashen lura da aikin soji a birnin Bagadaza ya fidda wata sanarwa dake cewa fafatawar da bangarorin biyu suka yi a kwanakin baya a yankin Abu Ghraib dake yamma da birnin na Bagadaza, ya baiwa sojojin dake marawa gwamnatin kasar damar sake kwace wasu unguwoyin yankin daga hannun dakarun na IS.
Kaza lika an ce sojojin gwamnatin sun hallaka mayaka 72 tare da lalata wasu motocin soji da mayakan kungiyar ta IS ke amfani da su a yankin.
A jihar Salahudin dake arewacin kasar kuwa, sojojin gwamnati da mayakan sa kai na 'yan Shi'a sun harbe dakarun kungiyar ta IS fiye da 10, tare da kwashe bama-bamai fiye da 100 da aka daddasa a gefen tituna. Kana sojojin gwamnatin kasar sun kwace garuruwa biyu dake da nisan kilomita 15 daga kudancin birnin Baiji.
A jihar Diyala dake gabashin kasar kuwa, yayin arangamar su da mayakan kungiyar ta IS, sojojin gwamnatin sun kwace wani muhimmin sansanin sojin kungiyar, sun kuma harbe 'yan gwagwarmayar su 37. (Zainab)