Sanarwar kuma ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kawancen yaki da kungiyar IS dake karkashin jagorantar kasar Amurka ya riga ya kai hare-haren sama kan garin Ayn al-Arab har sau 135, hakan ya hana kokarin da mayakan IS ke yi na shiga garin.
Dadin dadawa, an ba da labarin cewa, wani jami'in dakarun Kurdawa na kasar Sham ya bayyana a kwanan baya cewa, dakarunsa sun samu nasarar tsaron garin Ayn-al-Arab bisa taimakon da Amurka da sauran kasashe suka bayar kan kai farmaki daga sama. Da ma kungiyar IS ta mamaye yankunan garin kusan kashi 40 bisa 100 a baya, amma yanzu wannan adadi bai kai kashi 20 bisa dari ba. (Amina)