Shafin yanar gizo ta Intanet na hukumar tsaron kasar Faransa ya ba da sanarwa a ran 20 ga wata cewa, sojojin kasar sun sake kai hare haren sama kan na'urorin kungiyar IS dake kasar Iraqi, inda suka lalata motocin dakon kayayyaki na kungiyar guda biyu.
Sanarwar kuma ta nuna cewa, an kai wannan hari ne a yankin Tikriti mai tazarar kilomita 200 dake arewacin birnin Baghadaza hedkwatar kasar ta Iraqi, inda jiragen sama na yaki guda biyu na sojojin Faransa suka lalata motocin dakon kayayyaki masu nauyi na IS guda biyu a cikin wani matakin soja da suka dauka don taimakawa sojojin kasa na Iraqi. Ban da haka kuma, wadannan jiragen saman yaki biyu sun gudanar da aikin sintiri har na tsawon sa'o'i 8 a ran 19 ga wata. (Amina)