Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Iraki suka bayar, an ce, majalisar dokokin yankin Kurdawa mai cin gashin kansa na kasar Iraki ta zartas da wani kuduri a ranar 22 ga wata, inda ta bai wa gwamnatin yankin dama da iznin tura sojoji zuwa garin Ayn al-Arab na kasar Syria, wanda kungiyar IS take kokarin mamaye da kuma fafata yaki a kewayensa.
Gidan telebijin na kasar Iraki ya bayar da labarin cewa, bisa kudurin da majalisar yankin Kurdawa mai cin gashin kansa na kasar ta zartas a wannan rana da yamma, gwamnatin yankin za ta tura dakarunta masu dauke da manyan makamai zuwa garin Ayn al-Arab cikin hanzari don yaki da kungiyar IS.
Bugu da kari, shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a ranar 22 ga wata cewa, kasarsa za ta taimakawa dakarun yankin Kurdawa wajen shiga Ayn al-Arab don yaki da kungiyar IS. Amma kasar Turkiya ta ki amincewa da kasar Amurka da ta jefa makamai ga dakarun yankin ta jiragen sama. (Zainab)