Mistura wanda ya bayyana haka a yayin taron manema labaru da aka shirya a Geneva, ya yi gargadin cewa, yanzu yankin Kobane na cikin yanayi mai tsanani, sakamakon harin da kungiyar ISIS ke yi, idan kungiyar ta mamaye yankin, to mai yiwuwa ne za ta yi kisan gilla kan mutanen dake zama a wurin, da kuma wadanda ke yankunan dake dab da Kobane.
Mistura ya kara bayyana cewa, kamata ya yi, kasa da kasa su dauki matakan da suka dace bisa tushen girmama dokokin duniya, da mulkin kai da cikakken yankin kasar Syria don hana abkuwar irin masifa mai bakin ciki. (Bilkisu)