Bisa kididdigar da hukumar ta yi, ya nuna cewa mutanen da suka mutu a sakamakon hari sun hada da dakaru masu tsattsauran ra'ayi 374, da mayakan Kurdawa 268 da kuma fararen hula 20.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, wani jami'in mayakan Kurdawa na kasar Syria ya bayyana a ranar 16 ga wata cewa, bisa taimakon hari ta sama da kasar Amurka da sauran kasashen duniya suka bayar, dakarun Kurdawa sun samu nasara a yakin da suke na kare birnin Ayn al-Arab a kwanakin baya. Ya zuwa yanzu, kungiyar IS ta mallaki kasa da kashi 20 na birnin ne kawai. Jami'in ya kara da cewa, mayakan Kurdawa sun fara yunkurin kwato gabashi da kudu maso yammacin birnin. (Zainab)