A cikin sanarwar an ce, a 'yan kwanakin da suka wuce, kungiyar IS ta tayar da jerin farmaki a Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, da kuma jihohi da lardunan dake kewayensa, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutanen Iraki fiye da 10. Kwamitin sulhun ma ya yi zargi sosai kansu tare da jaddada cewa, za a gudanar da bincike kan wadanda suka keta dokokin jin kai na duniya, da take hakkin bil Adama a cikin kasar Iraki.
Haka zalika kwamitin sulhu ya sake nanata a cikin sanarwar cewa, dole ne za a cimma nasarar yaki da kungiyar IS, kuma akwai bukatar a yi namijin kokari don murkushe ayyukan ta'addanci bisa abubuwan da aka tanada cikin tsarin dokoki na MDD, kana da kawar da barazanar da suke kawowa zaman lafiya da tsaron duniya. (Bilkisu)