in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tura rukunin ba da horaswa kan aikin yaki da cutar Ebola
2014-11-09 20:45:23 cri

Rukunin farko na masu ba da horaswa kan aikin yaki da cutar Ebola ya tashi zuwa kasar Saliyo a safiyar ran 9 ga wata bisa tsarin da hukumar kiwon lafiya da kayyade iyali ta kasar Sin ta yi, domin baiwa kasashen yammacin Afrika wadanda suke fama da cutar taimako wajen horar da malaman aikin jiyya. Muhimmin aikin rukunin a wannan karo shi ne bullo da tsarin da za a bi a yammacin Afrika wajen horar da malaman aikin jiyya, ta yadda za a share fagen gudanar da aikin horaswa a nan gaba.

Wannan mataki da Sin ta dauka ya alamanta cewa, Sin ta fara tallafawa kasashen Afirka a aikin shawo kan cutar Ebola ta hanyoyi da dama a maimakon samar da tallafin jin kai kawai, kuma wannan ya kasance karo na 5 da Sin ta tura rukunin masananta zuwa yammacin Afrika.

Ya zuwa yanzu kuma, yawan masanan da Sin ta tura zuwa kasashen yammacin Afrika uku dake fama da cutar ya kai 252. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China