A gun bikin, Dja wanda ya wakilci gwamnatin kasarsa ta Guinea Bissau da nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin domin goyon baya da gudummawa da take bayarwa ga kasarsa a cikin dogon lokaci, ya ce, taimakon da kasar Sin ke samarwa ya kara kwarin gwiwwa ga gwamnatin kasar Guinea Bissau wajen tinkarar cutar Ebola, tare da kara karfin rigakafi da kuma shawo kan cutar.
A nasa bangare, Wang Hua ya bayyana cewa, a watan Afrilu na bana, bisa bukatun gwamnatin wucin gadi ta kasar Guinea Bissau, gwamnatin kasar Sin ta samar mata kayayyakin taimako da darajarsu ta kai Yuan miliyan 1 cikin gaggawa don rigakafin cutar Ebola. A wannan karo, kasar Sin ta kara samar da kayayyakin ba da kariya ga lafiyar jiki da sauran kayayyakin ba da agaji da darajarsu ta kai Yuan miliyan 5 ga kasar.
A cewar jakada Wang Hua, ko da yake ba a tarar da cutar Ebola a kasar Guinea Bissau a halin yanzu ba, amma ana fuskantar hali mai tsanani a wannan fanni a kasashen dake makwabtaka da ita. Don haka kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Guinea Bissau wajen kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa don taka muhimmiyar rawa wajen hana yaduwar cutar Ebola tare da shawo kan cutar a kasashe masu fama da cutar, har ma a dukkan duniya baki daya. (Zainab)