Bisa rahoton da hukumar ta gabatar, an ce, cutar Ebola ta kawo illa ga karfin gwamnatocin kasashen uku wajen kara samun kudin shiga, kana ta kara wa musu hadarin dogaro da taimako da basusuka daga kasashen waje. Gwamnatocin kasashen uku suna bukatar dala miliyan 328 don sake tafiyar da harkokinsu kamar yadda suka yi kafin zuwan cutar Ebola.
Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin tallafi dala miliyan 2 ga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO a ranar 5 ga wata a birnin Geneva don nuna goyon baya ga hukumar wajen taimakawa kasashen Guinea, Liberia da Saliyo kan yaki da cutar Ebola. (Zainab)