in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce za'a fara gwajin magungunan rigakafin ebola a yammacin Africa a watan Janairu
2014-11-07 17:13:17 cri
Hukumar samar da abinci ta MDD a ranar alhamis din nan ta sanar da cewar ya kamata a zage damtse wajen kokarin shawo kan cutar ebola don a samu nasara cikin sauri.

Kamar yadda hukumar lafiya ta MDD ta ke ganin idan an tabbatar da amincin shi, za'a samar da karin magungunan gwaji na rigakafi daga cutar zuwa ga kasashen da suka fi fama da ita a yammacin Africa nan da watan Januarun badi.

A Geneva a ranar alhamis din nan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi maraba da amincewar Swissmedic, hukumar kula da magunguna na kasar Switzerland don samar da maganin gwaji na rigakafin cutar ebola a karo na biyu.

Wannan maganin gwajin za'a gwada shi akan ma'aikatan kiwon lafiya da za su je aikin sa kai wadansu su da za'a dauka a matsayin ma'aikata kiwon lafiya a yaki da ake da cutar ta ebola a yammacin Afrika a cewar WHO.

A karin bayanin da aka yi tun da farko ranar laraba, hukumar ta bada rahoton cewa an samu mutane 13,042 masu cutar sannan 4,818 kuma ya zuwa yanzu sun mutu, inji Stephanne Dujjarick kakakin MDD da yake bayanin ga manema labarai a ranar alhmamis. Yace a matsayin da ake ciki na kasashen rahotannin mako mako na nuna cewa an samu daidaito a kasar Guinea. A Saliyo kuma rahoton makon na nuna cewa ana samun karuwar masu kamuwa da cutar, sannan a Liberiya bayanai na nuna cewa ana samun raguwar shi.

Sai dai kuma a duk kasashen 3, hukumar kiwon lafiyar ta duniya ta jaddada cewa cutar ta Ebola tana ci gaba da bazuwa da kara karfinta musamman a manyan biranen sannan kuma ana cigaba da bada karancin rahoto game da mutuwar mutanen da suka kamu da ita inji Dujjaric.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China