Darektan sashen kula da harkokin Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Songtian wanda ya sanar da hakan ya ce, kasar Sin ba za ta daina tallafawa kasashen na yammacin Afirka ba muddin ba a kawar da wannan cuta ba.
Ya zuwa yanzu kasar Sin ta tallafawa kasashen yammacin Afirka da ke fama da wannan cuta da agajin da ya kai dala miliyan 122.
A makon da ya gabata shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayar da sanarwar baiwa kasashen Liberia,Saliyo da Guinea da ke fama da cutar Ebola tallafin da ya kai dala miliyan 82.
Tun lokacin da cutar ta barke a watan Fabrairu, kasar Sin ta baiwa kasashen da ke fama da cutar ta Ebola a yammacin Afirka tallafi kashi 3, wadanda suka hada da watannin Afrilu, Agusta da kuma Satumba.(Ibrahim)