Hukumomin lafiya a Liberia sun sanar da raguwar wadanda ke kamuwa da cutar Ebola a kasar cikin 'yan makawannin baya bayan nan.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya Talata, ta rawaito mataimakin ministan ma'aikatar lafiyar kasar Tolbert Nyenswah, na cewa, duk da ci gaban da aka samu, mahukuntan kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba, wajen daukar karin matakan yaki da cutar.
Nyenswah wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da aka shirya, domin nazartar irin nasarar da ake samu game da yaki da cutar ta Ebola, ya kara da cewa, wajibi ne a dora bisa kwazon da ake yi, duba da cewa, harbuwar mutum guda na iya sake yada cutar ga al'umma masu yawa.
A daya hannun kuwa, shugabar kasar ta Liberia Ellen Johnson Sirleaf, da jagororin majalissun dokokin kasar sun alkawarta ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki, ciki hadda hukumomin kasashen ketare, wajen cimma nasarar aiwatar da shirin kota-kwana game da cutar, wanda zai kammala a ranar 12 ga watan nan na Nuwamba. (Saminu)