Cikin sanarwar da bankin duniya ya fidda, an ce, za a yi amfani da wadannan kudade don tallafawa kasashen wajen kafa wata cibiyar hadin gwiwa domin daidaita ayyukan yaki da annobar Ebola tsakanin MDD, hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa da kasashen uku da suka fi fama da cutar Ebola, haka kuma za a yi amfani da kudin wajen ba da horas ga masu aikin jinya.
Bisa rahoton da bankin duniya ya bayar, an ce, idan an kasa hana yaduwar cutar daga kasashen Guinea, Liberia da Saliyo zuwa kasashen dake kewayensu, to, ya zuwa karshen shekarar mai zuwa, lamarin zai janyo asara ga tattalin arzikin yammacin nahiyar Afirka wadda za ta kai kimanin dallar Amurka biliyan 32.6. (Maryam)