Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fid da wani sabon tsari, da ya tanaji inganta binne gawawwakin wadanda cutar Ebola ta hallaka.
Shirin dai ya tanaji bai wa iyalai da malaman addinan yankunan da cutar ta hallaka al'ummunsu, damar kasancewa cikin tsarin binne mamatan, tare da daukar matakan hana yaduwar cutar yayin da ake gudanar da shirye-shiryen binne su.
A cewar Pierre Formenty, daya daga kwararru a fannin hana yaduwar cutar Ebola na kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO, kimanin kaso 20 bisa dari na adadin wadanda ke kamuwa da ita, na harbuwa ne yayin da suke shirya mamatan. Don haka ya ce, abu ne da ya dace a inganta huldar dake tsakanin ma'aikatan lafiya, da malaman addinai domin kaucewa karuwar wannan matsala.
Sabon shirin dai na WHO ya tanaji daukar matakai daki-daki, na hana yaduwar Ebola yayin da ake gudanar da ayyukan da suka jibanci addini, da al'adu yayin binne irin wadannan mamata.
Kana an tsara baiwa masu ruwa da tsaki damar bayyana karin matakan da suka ga sun dace a dauka, ko gyara kan tsarin da WHOn ta fitar idan har akwai bukatar hakan. (Saminu)