in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria za ta tura masu aikin sa kai 506 zuwa kasashen dake fama da Ebola
2014-10-31 13:03:19 cri

Ministan kiwon lafiya na Nigeria, Khaliru Alhassan ya ce, nan ba da dadewa ba ne Nigeria za ta tura da masu aikin sa kai kimmani 506 zuwa kasashen da cutar Ebola ta yi kamari.

Ministan wanda ya bayyana wannan jawabin a lokacin taro na 57 na ma'akata kiwon lafiya na Nigeria a jihar Akwa-Ibom ya kuma ce, a karon farko za'a tura ma'aikatan sa kai 250 zuwa kasashen Liberia, Guinea da Saliyo domin a taimaka wajen dakusar da yaduwar cutar Ebola a Afrika ta yamma.

Alhassan ya kara da cewar, Nigeria za ta ci gaba da tabbatar da cewar, tana sanya ido a kan iyakokinta domin kaucewa shiga cikin hali na dar-dar.

Ministan ya bukaci jihohin kasar da su inganta kaimi wajen sa ido a kan iyakokinsu, tare da zamantowa masu sa ido a kan iyakokin Nigeria da kuma daukar mataki na kulawa da lafiyar duk wanda ya kamu da cutar.

Ministan ya ce, daga cikin mutane 2 'yan Nigeria mazauna birnin Free Town a kasar Saliyo wadanda suka kamu da cutar ta Ebola, daya daga ciki, an samu nasarar yi mashi magani, har ya warke, kuma daya mutumin yana karkashin killacewa ta kwanaki 21 a hannun kulawar cibiyar kebe jama'a ta kasar saliyo.

Ministan ya bukaci illahirin jihohin Nigeria da su zama a cikin shiri na inganta cibiyoyi na kebe jama'a saboda fuskantar duk wani kalubale game da cutar ta Ebola mai saurin kisan bil'adama, ko da yake hukumar lafiya ta duniya ta wanke Nigera daga jerin kasashe masu fama da matsalar Ebola. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China