in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na MDD ya yi kira da a ci gaba da kokarin shawo kan cutar Ebola
2014-11-01 16:55:16 cri
A jiya Jumma'a 31 ga watan Oktoba ne manzon musamman na MDD kan batun cutar Ebola David Nabarro, ya bayyana cewa ko da yake an sami sassauci a wasu wurare wajen yaduwar cutar Ebola, duk da hakan kamata ya yi a ci gaba da mai da hankali kan yaki da ake yi da yaduwar cutar.

Ya ce babu shakka akwai bukatar kasashen duniya, su ci gaba da kokari wajen shawo kan cutar yadda ya kamata.

David Nabarro ya kuma bayyana damuwarsa kan kebewar da wasu kasashe suke yiwa mutanen da suka dawo daga kasahsen dake fama da cutar ta Ebola, musamman ma ma'aikatan jiyya. Ya ce, har yanzu ana bukatar ma'aikatan jiyya sama da 1000 da zasu shiga yankunan da cutar ta Ebola ke addabar al'umma domin bada agaji, don haka kamata ya yi a rika karbar irin wadannan mutane hannu bibiyu yayin da suke dawowa kasashen su na ainihi.

A wani ci gaban kuma, jakadan Sin a kasar Saliyo Zhao Yanbo, ya rattaba hannu kan takardar kafa ofishin nazari kan kwayoyin halittu da Sin za ta aiwatar kyauta a kasar. Yayin bikin sanya hannu kan wannan aiki da ya gudana ran 30 ga watan Oktoba a birnin Freetown, fadar gwamnatin Saliyon, ministan kudin kasar Kaifalla Marah ne ya wakilci tsagin kasar sa.

Minista Marah ya jinjinawa kasar Sin bisa muhimmancin da take dorawa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Tuni dai ofishin nazari na tafi da gidanka da Sin ta baiwa Saliyon kyauta ya fara taimakawa wajen gwaje-gwajen jini, da gudummawa ga daukar matakai masu nagarta wajen shawo kan cutar Ebola. Kana ana sa ran sabon ofishin da Sin za ta kafa, zai taimakawa kasar wajen kyautata ikon ta na inganta kiwon lafiya, da shawo kan cututtuka dake iya yaduwa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China