Kayayyakin da Sin ta samar sun hada da rigunan kariya, tabarau na kariya da wasu na'urorin bincike kan cutar Ebola. An isar da kayayyakin zuwa birnin Brazzaville a wannan rana.
A gun bikin mikawar kayayyakin, jakadan Sin dake kasar Guan Jian ya bayyana cewa, kasar Sin ta yaba wa gwamnatin kasar Congo Brazzaville domin ta yi kokarin rigakafin cutar Ebola, kana ta yi kira ga kasa da kasa da su kara yin hadin gwiwa don taimakawa kasashe masu fama da cutar Ebola wajen yaki da cutar.
A nasa bangare, ministan kiwon lafiya na kasar Congo Brazzaville Francois Ibovi ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin domin ta ba da gudummawa ga kasarsa, kana ya ce, kasar Sin ta cika alkawarinta na ba da kayayyakin gudummawa, kuma ta kai kayayyakin zuwa kasarsa cikin lokaci. (Zainab)