Har ila yau a yayin taron manema, Mr. Hong ya yi bayani kan yadda kasar Sin take samar wa kasashen Afirka taimako wajen yaki da cutar, inda ya ce, kasar ta fara taimakawa wasu kasashen tun barkewar cutar ba tare da bata lokaci ba. Ya ce ya zuwa yanzu kuma, Sin na ci gaba da taimaka musu kan aikin, ta riga ta aike da masanan kiwon lafiya zuwa kasashen dake fama da cutar da kuma samar musu kayayyakin agaji sau da dama. Bugu da kari, kasar Sin ta samar da manyan fasahohi guda biyar game da yadda take bayar taimako kan yaki da cutar Ebola yadda ya kamata, na farko shi ne, tana gudanar da ayyukan ba da taimako cikin sauri, na biyu shi ne, tana tsayawa tsayin daka wajen fuskantar da cutar tare da jama'ar Afirka dake fama da ita, na uku shi ne, tana mai da hankali kan yadda za ta iya gudanar da ayyukan ba da taimako a kasashen Afirka yadda ya kamata, na hudu shi ne, ayyukan agaji da kasar Sin ke aiwatar na kunshi da yankuna da dama, na karshe shi ne, tana mai da hankali kan yadda za a iya kawar da cutar a Afirka daga tushe.
Hong Lei ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta dakatar da ayyukan taimakonta a kasashen Afirka ba, sai har an kawo karshen cutar Ebola a duk fadin nahiyar, sannan za ta ci gaba da taimaka wa kasashe da jama'ar Afirka domin cimma nasarar yaki da cutar tun da wuri. (Maryam)