Wannan dai shi ne karo na uku da kasar Sin ta aike da kayayyakin agaji zuwa Afirka. Wadannan kayayyaki dai sun hada da tufafin kariya, da na'urar auna zafin jiki da dai sauransu.
Jakadan kasar Sin dake kasar Senegal Xia Huang ya bayyana cewa, hakan na cikin muhimman matakai da kasar Sin ke dauka wajen taimaka wa kasashen dake fama da cutar, kuma tallafin zai ba da taimako matuka ga gwamnatin kasar ta Senegal game da hana yaduwar cutar Ebola a kasar. (Maryam)