A wannan rana a gun taron manema labaru, John Kirby ya bayyana cewa, a ranar 7 da 8 ga wata, Amurka da aminanta sun kai hare hare ta sama sau shida kan kungiyar ISIS dake kudanci da kudu maso yammacin birnin Kobane na Syria, hakan ya lalace wasu makamai da kayayyakin na'urorin soja na ISIS, tare da tilastawa dakarun kungiyar janye wa daga wannan yanki. Amma a sa'i daya ya jaddada cewa, idan babu taimakon sojojin kasa, to akwai wuya a ceci Kobane ta hanyar kai hare haren jirgin yaki ta sama kawai. Ke nan akwai yi yuwar rasa wannan birni da sauran garuruwasu.
John Kirby ya kara da cewa, kafa da horar da wata rundunar soja a Syria za ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da kungiyar ISIS.
A ranar 7 ga wata, firaministan Turkiya ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su kai hari ta kasa kan kungiyar ISIS, tare da ba da shawarar kafa yankin hana zirga zirgar jirgin sama da yankin sassauci a iyakar kasa tsakanin Syria da Turkiya. A jiya sakataren harkokin waje na Amurka da takwaransa na Birtaniya sun bayyana cewa, kamata ya yi a yi la'akari da wannan shawarar Turkiya.(Fatima)