A jiya ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da cewa, an samu lafawar cutar ebola a kasar ta Laberiya, inda yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya ragu sosai.
Jaridar New York Times ta ba da labari a jiya Laraba 29 ga wata cewa, mataimakin babban jami'n hukumar Bruce Aylward ya bayyana a wannan rana a birnin Geneva cewa, yawan mutanen da suke kamuwa da cutar yana raguwa a kasar Laberiya, cibiyar da ke ba da jiyyar cutar a Monrovia wadda a baya ke cike da mutane, yauzu har an fara samun gadajen da ba marasa lafiya a kansu, haka kuma yawan gawarwaki da hukumomi da abin ya shafa suke karba sakamakon cutar ya ragu.
Duk da haka kuma, Aylward ya yi nuni da cewa, Ebola cuta ce mai hadari dake saurin kashe mutane, kuma har yanzu ba a tabbatar da cewa an shawo kan cutar a Laberiya ba. Don haka kamata ya yi a ci gaba da mai da hankali kan matakan yaki da cutar. (Amina)