Wakilin babban sakatare janar na MDD, kana shugaban shirin yaki da cutar Ebola na MDD (UNMEER) Anthony Banbury ya gana da shugabannin kasashen Guinea, Saliyo da Liberia, yayin da ake kokarin kawo karshen annobar cutar Ebola a yammacin Afirka.
Wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ta kuma bayyana cewa, Mr. Anthony Banbury ya kuma gana da abokan hulda na kasa da na katare, kana ya ziyarci cibiyoyin lafiya da ake kan ginawa don gane wa idonsa irin ci gaban da aka samu a kokarin da ake na hana yaduwar cutar.
Ganawar bangarorin biyu ta mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da taimakon da kasashen duniya ke bayar wa yadda ya kamata a kokarin da ake na dakile yaduwar cutar ta Ebola.
Bugu da kari, ganawar za ta baiwa wakilin na MDD damar sanin halin da kowace kasa ke ciki da kuma irin agajin da take bukata.
Ya zuwa yanzu cutar Ebola ta halaka mutane sama da 4,000 a kasashen Guinea, Saliyo da kuma Liberia daga cikin mutane sama da 8,900 da suka kamu da cutar. (Ibrahim)