in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci hadin kan sarakunan gargajiya wajen yaki da Ebola a Saliyo
2014-10-30 09:54:24 cri

Mazauna yankin arewacin kasar Saliyo sun yi maraba da sakon shugaba Koroma inda ya yi kira ga sarakunan gargajiya na yankin da su ba da hadin kai wajen yaki da cutar Ebola a yankunan masarautunsu, kuma rashin yin haka din zai kai su ga rasa mukaminsu. Shugaban kasar Saliyo dake ziyarar gani da ido a yankin arewacin kasar a wannan makon, ya nuna rashin jin dadinsa da kuma damuwarsa kan sakaci da rashin iya aiki na shugabannin gargajiya, musammun ma sarakuna, shugabannin addinai da wakilan jama'a, kan yadda suke gudanar da kokarin yaki da cutar Ebola bayan dukkan matakan da gwamnatin kasar ta dauka na kawar da wannan cuta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China