in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya zai tallafa wa masu aikin sa kai kan Ebola na Kenya
2014-10-29 14:34:22 cri

Shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim, ya ce, bankin duniya zai baiwa masu gudanar da ayyukan sa kai na kasar Kenya tallafin kudi domin su aiwatar da alkawarin da suka yi na bulaguro zuwa kasashen Afrika ta yamma inda ake fama da matsalar barkewar cutar Ebola da zimmar dakusar da yaduwar cutar.

Kasar Kenya ta zamanto abin koyi musamman saboda ci gaban da ta samu a fannin gudanar da ayyukan kiwon lafiya.

A kalla mutane 'yan kasar Kenya dari 6 ne suka sadaukar da kansu, tashi daga kasarsu zuwa Afrika ta yamma, domin taimakawa wajen dakusar da yaduwar cutar Ebola a kasashen dake yanki.

Darektan harkokin kiwon lafiyar Kenya Nicholasa Muraguri ya bayyana cewar, daga cikin mutane masu gudanar da ayyukan sa kan, akwai masu aikin kula da marasa lafiya da likitoci.

Maraguri ya ce, za'a yi amfani da kudade wajen sa ido, da kuma aiwatar da gwaje-gwaje na cututtuka da kuma kula da wadanda suka kamu da cutar, tare da gudanar da kamfe din wayar da kan jama'a a kan cutar Ebola mai saurin kashe bil'adama.

Alkaluman kididdiga na nuni da cewar, hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta cewar, adadin wadanda suka kamu da cutar sun kai kimanin 9936 kuma daga ciki, mutane 4,877 sun mutu a sakamakon cutar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China