in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin agazawa Afirka ta hanyoyin wucin gadi da na din din din wajen yaki da cutar Ebola
2014-10-25 16:50:50 cri

Ranar 24 ga wata, Liu Jieyi, zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD ya yi wa kafofin yada labaru da ke MDD karin bayani game da yadda gwamnatin Sin za ta tallafa wa kasashen yammacin Afirka a zagaye na hudu wajen yaki da annobar cutar Ebola.

Mista Liu ya ce, kasar Sin za ta inganta tuntuba da yin mu'amala da MDD da hukumar kiwon lafiyar ta kasa da kasa WHO, za ta kuma halarci taron da kawancen yaki da annobar a duk fadin duniya na MDD ya kan shirya. Har wa yau kasar Sin za ta hada kai da kasar Amurka da sauran kasashe masu ruwa da tsaki a fannonin tantance yaduwar annobar, horas da ma'aikata, yin bincike da ba da jinya, yin amfani da bayanai da dai sauransu, amma akwai sharadi na farko, wato nuna girmama sosai ga kasashen da ke samun taimakon.

Haka zalika, a cewar Liu Jieyi, kasar Sin za ta ba wa yankunan da ke yaki da annobar kayayyakin taimakon da suke matukar bukata, kamar gadaje, na'urar ba da kariya da dai sauransu. Sin za ta kafa wata cibiyar ba da jinya a kasar Saliyo da take fi fama da annobar. Sa'an nan karin masanan kiwon lafiya za su je yankunan da ke yaki da annobar, inda za su ba da jagoranci wajen kyautata shirin ayyukan gwamnati na yaki da annobar. Za a kara aika da ma'aikatan lafiya domin horas da takwarorinsu na wurin. Ban da haka kuma, kasar Sin za ta kaddamar da shirin yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Afirka ta fuskar kiwon lafiyar al'umma.

Kasar Sin za ta karfafa karfin agazawa kasashen Afirka wajen yaki da annobar cutar Ebola zagaye na hudu, za ta kuma kyautata tallafawar da take bayarwa, za ta juya hankalinta zuwa ba da jinya, yin rigakafin cutar da kafa tsarin tsaron lafiyar al'umma, a maimakon ba da agajin jin kai cikin gaggawa, a kokarin taimakawa kasashen da ke yaki da cutar ta hanyoyin wucin gadi da na din din din don su inganta karfinsu da kafa tsarin din din din na tinkarar annoba, in ji mista Liu.

Har ila yau kuma, madam Marie-Paule Gini, mai ba da taimako ga babbar darektar WHO ta bayyana a ranar 24 ga wata a birnin Geneva cewa, mai yiwuwa ne za a fara aiki da alluran yin rigakafin annobar cutar Ebola fiye da dubu 10 a farkon rabin shekara mai zuwa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China