in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta kafa wani shirin kasa na yaki da cutar Ebola
2014-10-24 13:18:36 cri

Kasar Najeriya ta sanar a ranar Alhamis cewa, ta kafa wani shirin kasa kan cutar Ebola (NEPP) domin sanya ido ga duk wata annobar wannan cuta a nan gaba a cikin kasar dake yammacin Afrika.

A ranar Litinin, hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa, Najeriya ta fita daga kasashen dake fama da cutar Ebola, ba'a samu wani ba da ya kamu da cutar Ebola a tsawon makwanni shida na baya bayan nan, amma hukumomin kasar sun dauki niyyar tsaya cikin shirin ko ta kwana wajen yaki da cutar Ebola dake da karfin yaduwa.

Wannan sakamako da hukumomin kiwon lafiya na Najeriya suka cimma ba zai ba mu damar yin barci har da nasara ba. Wannan zai kasance wani kashedi cewa, annobar cutar Ebola ta yanzu na cigaba da zama barazana ga Najeriya da duniya baki daya, in ji Khaliru Alhassan, babban jami'i a ma'aikatar kiwon lafiya a cikin wata hira tare da 'yan jarida a birnin Abujan Najeriya. Idan har ba'a killace da kawar da cutar Ebola daga dukkan kasashe ba, musammun ma a shiyyar yammacin Afrika, to Ebola za ta cigaba da kasancewa wata bazarana ga Najeriya, in ji wannan jami'i.

A cikin tsarin wannan shirin yaki da cutar Ebola, gwamnatin Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afrika za ta kafa wata cibiyar kasa kan ayyukan gaggawa a birnin Abuja, da haka kuma za a fadakar da jama'a kan cutar tare da kara yawan asibitoci da jami'an lafiya a kasar, in ji mista Alhassan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China