Gwamnatin kasar Mauritaniya ta dauki niyya a ranar Asabar tna rufe kan iyakarta da kasar Mali domin yin rigakafi kan yaduwar cutar Ebola. An gano dai mutum mace tna farko a ranar Alhamis da ya ta kamu da cutar Ebola a Kayes, wani birnin dake yammacin kasar Mali. Wannan kuma wata karamar yarinya ce mai shekaru biyu da aifuwa da ta fito daga garin Kissidougou na kasar Guinee, wadnda kuma ta rasu a ranar Jumma'a.
Hukumomin Nouakchott sun bada umurnin rufe dukkan hanyoyin shige da ficen jama'a dake kan iyaka da kasar Mali domin kaucewa duk wata kamuwa al'ummomin kasar Mauritaniya da cutar Ebola in ji dokta Liman Deddeh, babban jami'in lafiya na birnin Kobonni dake kan iyaka, mai tazarar kilomita fiye da dubu daya daga Nouakchott, babban birnin kasar Mauritaniya. (Maman Ada)