in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Sin na kokarin taimakawa kasashen yammacin Afrika wajen yaki da cutar Ebola
2014-10-30 20:44:02 cri

Kakakin hukumar tsaron kasar Sin Yang Yujun ya shedawa manema labaru a yau Alhamis 30 ga wata cewa, kamar yadda kasar Sin ta tsara, sojojinta na taimakawa kasashen yammacin Afrika wajen yaki da cutar Ebola.

Mr. Yang ya ce, tun daga farkon watan Satumban da ya gabata, sojoji masu aikin jiyya 30 daga asibitin rundunar soja ta 302, suka tafi kasar Saliyo don gudanar da aikin baiwa wadanda suka kamu da cutar jiyya. A cewarsa, kwanan nan, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar ba da taimakon gina wata cibiyar ba da jiyya mai gadajen kwantar da marasa lafiya 100 a Laberiya, don kulawa da wadanda suka kamu da cutar, kuma sojojin kasar Sin ne suke daukar nauyin aiwatar da wannan aiki, yanzu ana kokarin gina wannan cibiya.

Ban da haka kuma, sojojin kasar Sin za su tura masana da kwararru kan yaki da annoba zuwa Laberiya domin ba da gudummawa da horaswa, sannan kuma, sojojin za su dauki nauyin tattara kayayyakin jin kai da sufurinsu zuwa kasahen yammacin Afrika. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China