Sanarwar ta bayyana cewa, wannan yarinya mai shekaru biyu da haihuwa ta zo daga kasar Guinea. Bisa binciken jinin da aka yi mata a ranar 23 ga wata,, an tabbatar da cewa, ta kamu da cutar Ebola. Yanzu an killace ta a wani asibitin dake birnin Kayes don yin mata jinya, kana an killace mutanen da suka yi mu'amala da ita. Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Mali ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don hana yaduwar cutar Ebola a kasar.
Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta yi, an ce, ya zuwa yanzu, mutane 4877 sun mutu sakamakon cutar Ebola a duniya, yayin da mutane 9936 ke kamuwa da cutar. Kasashen Guinea, Saliyo da Liberia da ke yammacin Afirka kuwa suna cikin hali mai tsanani wajen yaki da cutar.
Bugu da kari, WHO ta bayyana cewa, aikin gaban kome a yanzu shi ne hana yaduwar cutar Ebola a wadannan kasashe 3 na yammacin Afirka, wannan kuwa shi ne mataki mafi muhimmanci na hana yaduwar cutar a fadin duniya. (Zainab)