An nuna cewa, kKasashen Guinea da Saliyo da Liberia dake yammacin nahiyar Afirka sun fi fama da cutar Ebola, kuma mafi yawan mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola sun fito daga wadannan kasashe uku.
Bisa wani labari mai dumi dumi da aka bayar, an ce, yarinyar da aka tabbatar da kamuwa da cutar Ebola ta farko a Mali ta rasu. Kuma tuni gwamnatin kasar Mali ta shelanta cewa, yarinyar tare da iyalinta sun dawo daga wata ziyara a kasar Guinea. Yanzu an riga an kebe mutane sama da 40 da suka taba mu'amala da wannan yarinya zuwa wani wuri na daban.
Kungiyar WHO ta yi gargadi cewa, mai yiyuwa ne yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola ya zai kara karuwa a nan gaba.(Fatima)