in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar Liberia ta jinjinawa kasar Sin bisa gudummawarta a yaki da cutar Ebola
2014-10-29 10:50:43 cri
Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta jinjinawa namijin kokarin da kasar Sin take yi, wajen ba da agaji ga yakin da ake yi da cutar Ebola, musamman a kasar Liberia, daya daga kasashen da cutar ta fi kamari.

Sirleaf wadda ta yi wannan yabo yayin ganawarta da Mr. Zhang Jiang, shugaban tawagar share-fage gina cibiyar kasar Sin ta ba da jinya ga masu dauke da cutar Ebola, ta ce, wannan cuta ta Ebola ta haifar da babbar illa ga bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma.

Shugabar kasar Liberia ta kara da cewa, Sin ta samar da gudummawa mai tarin yawa, ita ce kuma kasa ta farko da ta tura jiragen saman musamman don jigilar kayayyakin tallafi, ta kuma jagoranci ayyukan ba da gudummawa ta kasa da kasa.

Kaza lika Sirleaf ta ce, kasarta na fatan tawagar share-fagen na kasar Sin za ta gudanar da ayyukanta cikin sauri, a kokarin kammala gina cibiyar jinya ga masu dauke da cutar ta Ebola a kasar cikin hanzari, inda za ta karbi masu dauke da cutar.

Bugu da kari, Sirleaf ta bayyana Sin a matsayin muhimmiyar kawa ga Liberia a fannin kiwon lafiya, tana mai fatan likitocin kasar Sin za su shiga Liberia, domin ba da karin horo ga likitocin kasar, tare da karfafa musu gwiwa wajen bunkasa tsarin kiwon lafiyar al'ummar kasar.

Shi kuwa a nasa jawabi, jakadan Sin dake kasar ta Liberia Zhang Yue cewa ya yi, matakan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a kwanakin baya, game da samar da sabuwar hanyar ba da gudummawa ga kasashen yammacin Afirka ciki har da kasar ta Liberia, sun kunshi nazari kan halin da ake ciki a kasashe masu fama da cutar Ebola, kuma hakan zai taimakawa kokarin samar da kayayyakin tallafi da tura likitoci.

Ya ce, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin gina cibiyar aikin jinya ga masu fama da cutar Ebola mai kunshe da gadaje 100 a kasar Liberia, za kuma a tura likitoci zuwa cibiyar don gudanar da aiki. Aikin da zai zamo irinsa a farko da wata kasa za ta gudanar.

Tuni dai wannan tawaga ta share-fage daga kasar Sin, wadda za ta taimakawa aikin ginin wannan cibiya ta isa kasar Liberia, za ta kuma kama aikin gadan-gadan. Aikin da kuma ake fatan kammalarsa cikin kankanen lokaci domin fara karbar masu fama da cutar ta Ebola. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China