Annobar cutar Ebola dake nata zamani a wasu kasashen yammacin Afrika ba za ta kawo illa sosai ba ga tattalin arzikin Liberiya, Guinea da kuma Saliyo, amma za'a samu hadari karami kan ci gaban nahiyar a dunkule, in ji wani babban jami'in asusun ba da lamuni na duniya IMF reshen Afrika a ranar Alhamis.
A yayin wani taron manema labarai, bayan gabatar da hasashen tattalin arzikin shiyyoyi na shekarar 2014 na IMF na kasashen nahiyar Afrika dake kudu da hamadar Sahara a birnin Harare, darekta IMF reshen Afrika, Antoinette Sayeh, ta bayyana cewa, kasashen nan uku da suka fi fama da cutar Ebola, da GDP yake wakiltar kashi daya cikin dari kawai da na sauran duk Afrika, ba ya da sa'ar kawo babban sauyi ga bunkasuwar nahiyar, da zai wuce, a cewar hasashen IMF, da kashi 5 cikin 100 a shekarar 2014 zuwa kashi 5,8 cikin dari a shekakar 2015.
A cewar madam Sayeh, hasashen bunkasuwa na IMF ya yi la'akari da duk wata matsala idan har cutar Ebola ta ci gaba da yaduwa har zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.
Haka kuma jami'ar ta ba da shawarar kan daukar matakan gaggawa cikin hadin gwiwa domin killace cutar da kuma rage illarta kan tattalin arziki a cikin shiyyar dake samun cigaba mai karfi tun yau da 'yan shekaru. (Maman Ada)