Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Liberia Sylvester Grigsby da wasu manyan jami'an kasar da kuma jakadan Sin dake kasar Liberia Zhang Yue ne suka tarbi jirgin saman dake dauke da kayayyakin a filin jiragen sama na Monrovia
Ban da wannan kuma, a ranar 29 ga wata, wasu karin jiragen sama guda biyu za su isa kasar ta Liberia, dukkan jiragen saman uku za su yi jigilar kayayyakin gini, na'urori da kuma magunguna da nauyinsu ya kai ton 253 gaba daya.
Mr Grigsby ya bayyana cewa, yayin da cutar Ebola take yaduwa a kasar Liberia da sauran kasashen yammacin Afirka, kasar Sin ta kara samar da babban taimako ga kasashen ciki har da kasar Liberia, wannan ya taimakawa kasar Liberia da sauran kasashe masu fama da cutar Ebola a Afirka, gwamnatin kasar Liberia da jama'arta ba za su manta da taimakon da kasar Sin ta ba ta ba. (Zainab)