in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya bayyana damuwa game da matakan da ake dauka kan ma'aikatan lafiya daga kasashe masu fama da Ebola
2014-10-28 10:23:47 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana rashin gamsuwa game da yadda ake daukar tsauraran matakan bincike, kan jami'an lafiya da ke komawa gida, bayan gudanar da aikin tallafi a kasashen dake fama da cutar Ebola.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric, ya ce, daukar matakan killace irin wadannan ma'aikata da zarar sun isa gida, wani nauyin takurawa ne ga wadanda suke ba da gudummawa ga dakile yaduwar cutar.

Tsokacin babban magatakardar MDDr dai na zuwa ne bayan da ma'aikaciyar lafiyar nan Baamurkiya Kaci Hickox, ta yi korafin cewa, an killace ta a wani tanti dake wajen asibitin filin jirgin saman Newark na birnin New Jersey tsakanin ranar Juma'a zuwa Litinin, bayan dawowar ta daga aikin ba da agajin jin kai a kasar Saliyo.

Da yake karin haske game da hakan, Ban ya ce, hanya daya tilo ta dakile yaduwar wannan cuta ita ce zage damtse, wajen shawo kan cutar tun daga tushe, musamman a kasashen da ta fi kamari. Ya ce, cutar Ebola barazana ce ga duniya baki daya, don haka ya zama wajibi a dauki matakai na bai daya domin yaki da ita.

Tuni dai wannan cuta ta Ebola ta hallaka dubban mutane a wasu kasahen dake yammacin Afirka, ciki hadda ma'aikatan lafiya 244, cikin ma'aikatan jiyya da likitoci 450 da aka hakikance sun harbu da ita. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China