Sun Jiwen ya yi jawabi kan halin da ake ciki dangane da matakan samar da kayayyakin taimakon rigakafi da yaki da cutar Ebola zagaye na uku ga kasashen Afirka da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar. Sun ya bayyana cewa, a halin yanzu, jiragen saman da za su yi dakon kayayyakin da kasar Sin ta bayar sun tashi da karfe 3 da minti 12 na safiyar yau Litinin daga filin jirgin saman birnin Tianjin zuwa kasashe shida na Afirka ciki har da kasar Mali, kuma jirgin saman da zai je kasar Nijeriya ya riga ya tashi daga birnin Beijing. Kayayyakin da za a yi jigilarsu a wannan karo sun hada da rigunan kafiya, tabarau na kariya, na'urorin binciken zafin jiki da dai sauransu. (Zainab)