Shugaban kasar Amurka Obama ya ce, ya kamata ma'aikatan kula da lafiyar jama'a da suka koma gida Amurka, a dauki mataki na jinjina musu tare da kaucewa duk abin da zai yi sanadiyyar juya baya ga Afrika ta yamma domin a samu a tallafawa wadanda suka kamu da cutar ta Ebola.
Shugaban kasar ta Amurka ya yi wannan jawabin ne bayan jihohin New York, New Jersey da sauran jihohin Amurka sun bullo da dokoki na killace ma'aikatan lafiya a bisa tilas, a inda hakan ya kawo ka ce-na ce daga bangaren kwararrun kiwon lafiya.
Obama ya ce, Amurka ba ta da muradin haramtawa ma'aikatanta zuwa Afrika ta yamma domin taimakawa wadanda suka kamu da cutar.
Obama ya ce, ya kamata Amurka ta dauki mataki da yake la'akari da bayanai na kimiyya da kuma kwarewa a maimakon amfani da jita-jita. (Suwaiba)