An ba da labari cewa, an gano mutum na farko da ake tababa kamuwa da cutar, wanda daga bisani aka tabbata bai kamu da wannan cuta ba. Dangane da hakan, akwai dan jarida da ya tambaya shin mene ne ra'ayin kasar Sin kuma wane irin matakai ta dauka wajen yin rigakafin cutar, kuma ko Sin ta gano wadanda ake tababa kamuwa da cutar a kasar.
Mr. Hong ya ce, wannan matsala ya zama wani kalubale ga daukacin duniya yanzu, don haka Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasa da kasa don taimakawa kasashen Afrika wajen magance cutar. Ya kara da cewa Sin ta samar wa Afrika babban tallafi, har ma shugaba Xi Jinping ya sanar da shirin samar da tallafi zagaye na hudu a makon da ya gabata, an yi imani cewa, wadannan matakai za su taka muhimmiyar rawa wajen yaki da Ebola a Afrika.
Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Sin na yin iyakacin kokarin gudanar da aikin yin rigakafi. Ciki hadda bincike zafin jikin wadanda suka shiga cikin kasar, tare da samar da horo kan matakan da za a dauka in cutar ta zo a wasu wurare. Ta wadannan matakai, ba a gano wani da ya kamu da cutar a kasar ba don haka za a ci gaba da wannan aiki yadda ya kamata. (Amina)