in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gudummawar da kasar Sin ta samar a zagaye na hudu na yaki da cutar Ebola na shafar fannoni shida
2014-10-29 15:33:02 cri
A 'yan kwanakin baya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da ba da gudummawar yaki da cutar Ebola zagaye na hudu, ga kasashen Afirka masu fama da cutar da yawansu ya kai kudin kasar Sin Yuan miliyan 500. Game da hakan, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Sun Jiwen ya bayyana a ranar 29 ga wata cewa, wannan gudummawa tana shafar fannoni shida.

Na farko shi ne tura tawagogin masanan kiwon lafiya ga kasashen Liberia, Saliyo da Guinea, don taimakawa da shiga aikin kandagarki, da na yaki da cutar Ebola a kasashen uku, kana an tura likitoci zuwa kasashen 3 don taimakawa wajen horar da likitocin kasashen.

Na biyu shi ne ci gaba da samar da kayayyakin gudummawa, ciki har da gadaje, da motoci, da na'urorin kariya da dai sauransu, da kara taimakawa kasashen uku wajen daga karfin karbar wadanda suka kamu da cutar, da jigilarsu zuwa asibitoci daban daban, da kuma tsaftace ababen da ka iya yada cutar, da kuma killace kayayyakin amfanin likitoci da aka gama amfani da su.

Na uku kuma shi ne taimakawa Liberia wajen gina cibiyar ba da jinya ga masu dauke da cutar Ebola mai kunshe da gadaje 100, da tura likitoci 160 don gudanar da aiki a cibiyar.

Na hudu shi ne ba da kudin agaji dala miliyan 6 ga asusun yaki da cutar Ebola na MDD.

Na biyar kuwa shi ne kaddamar da shirin hadin gwiwa kan kiwon lafiya a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da ba da horo ga kasashen uku mafiya fama da cutar Ebola, da kungiyar AU da ECOWAS da sauran kasashen Afirka har sau 12 a shekarar 2015, da fara yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka wajen nazarin cututtuka masu yaduwa, da tura masana da su shiga aikin gina cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta Afirka karkashin kungiyar AU.

Na shida shi ne kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da halartar taron tawagar musamman ta tinkarar cutar Ebola ta MDD, da tura jami'ai da ma shiga tawagar ta musamman. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China